Babu rashin jituwa tsakanina da Ronaldo — Bale

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gareth Bale ya ce 'yan jarida ne ke son haɗa shi faɗa da Ronaldo.

Gareth Bale ya ce babu wata rashin jituwa tsakaninsa da takwaransa na kulob ɗin Real Madrid Cristiano Ronaldo.

A shekarar da ta wuce ne aka yi ta watsa jita-jita cewa akwai 'yar tsama tsakanin 'yan wasan biyu, inda aka yi ta sukar Bale.

Amma Ronaldo ya kare Bale, wanda shi ma ya ce babu rashin jituwa a tsakaninsu, gabanin fafatawar da za su yi da Manchester City a gasar cin Kofin Zakarun Turai.

Bale ya ce, "Mun sha nanatawa cewa babu wata matsala a tsakaninmu. Muna ɗasawa da juna; 'yan jarida ne kawai suke so su hada mu faɗa".

Dan wasan ya kara da cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne su murza leda, sannan su lashe kofunan gasar da ke gabansu.