Satar fasaha na barazana ga fina-finan Hausa

Hakkin mallakar hoto Hafizu Bello

Kungiyar masu shirya fina-finan Hausa na arewacin Najeriya ta ce tana fuskantar kalubale sosai na satar fasaha.

Shugaban kungiyar, Salisu Muhammad Officer, ya kara da cewa suna fuskantar wannan matsala ne ta bangaren wakoki da kuma fina-finan na Hausa.

A wata hira da wakilinmu Mohammad Kabir Mohammad ya yi da shugaban kungiyar shirya fina-finan Hausa na arewacin Najeriya, ya yi karin bayani a kan irin kalubalen da suke fuskanta:

Ya kara da cewa mai shirya fina-finai na samun kashi 30 ne kawai cikin 100, inda satar fasaha ke kwashe ragowar kashi 70 din.

Ana zargin kungiyar da satar fasaha daga masu shirya fina-finai a indiya, musamman abin da ya shafi labari da waka.

Sai dai Muhammad Officer ya musanta wannan zargin.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti