'Yan tawayen Libya sun fara fitar da fetur

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Tattalin arzikin Libya ya dogara ne kacokan kan fetur.

Daya daga cikin gwamnatocin 'yan tawayen Libya ta fara safarar man fetur dinta zuwa kasashen waje, a wani mataki na bijirewa hukumomin da ke Tripoli, babban birnin kasar.

Gwamnatin 'yan tawayen, wacce ke da cibiya a gabashin kasar, ta kafa kamfanin man fetur dinta a shekarar da ta wuce domin yin adawa da gwamnatin da ke Tripoli, wacce kasashen duniya suka amince da ita.

Sai dai ba ta fara sayar da fetur ba sai a yanzu.

Tattalin arzikin Libya ya dogara ne kacokan kan fetur, sai dai rikicin siyasar da ake yi a kasar da rashin tsaro sun tilastawa kasar rage man da take fitarwa, bayan kifar da gwamnatin Moammar Gaddafi.

A watan jiya ne gwamnatin da kasashen duniya ke mara wa baya ta koma birnin Tripoli da zama.