Mitsubishi ya dade yana yin kuskure

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugabannin kamfanin sun amince da tafka kuskure.

Kamfanin kera motoci na Mitsubishi ya amince cewa tun daga shekarar 1991 yake tafka kuskure a tsarinsa na auna yawan fetur din da motocinsa ke sha.

Hakan ya faru ne bayan wani rahoto da ya fito a makon jiya, wanda ke cewa kamfanin ya amince cewa ya yi karya a bayanan da ya bayar na yawan man da motoci 600,000 ya da sayar a Japan ke sha.

Mataimakin shugaban kamfanin Ryugo Nakao ya shaida wa wani taron manema labarai a birnin Tokyo ranar Talata cewa, "Mun yi ta tafka irin wannan kuskure tun daga shekarar 1991".

Sai dai bai bayyana yawan motocin da lamarin ya shafa ba.

Shugaban kamfanin, Tetsuro Aikawa, ya ce ana ci gaba da yin bincike kan lamarin, yana mai cewa mai yiwuwa a sake gano wasu matsalolin.

Hannayen jarin kamfanin sun sake faduwa da kashi goma cikin dari a Tokyo, inda yanzu hannayen jarin suka fadi da kashi 50 cikin 100 jimulla.