An bukaci Saraki ya sauka daga mulki

Image caption Ana tuhumar Saraki da zargin yin karya wajen bayyana kadarorinsa.

Daruruwan masu zanga-zanga a Najeriya sun yi wa majaliasar dokokin kasar tsinke, inda suka bukaci shugabanta Sanata Bukola Saraki ya sauka daga mulki.

Masu zanga-zangar, wadanda suka fara tattaki daga dandalin Unity Fountain da ke tsakiyar Abuja, babban birnin kasar, suna rike da kwalaye da aka rubuta da aka rubuta "Dole Saraki ya sauka", da "Mun gaji da Saraki", da sauransu.

Masu zanga-zangar, wadanda suka hada da kungiyoyin fararen hula da na dalibai, sun kuma zargi 'yan majaliasar dokokin da yin kafar-ungulu a yunkurin shugaban kasar Muhammadu Buhari na kawo sauyi a kasar.

Sun bukace su da su yi gaggawar yin gyare-gyare a kasafin kudin kasar domin shugaban ya sanya masa hannu.

Ana dai tuhumar Sanata Saraki da laifuka 13 wadanda suka hada da yin karya wajen bayyana kadarorinsa, ko da ya ke ya musanta zargin.

Idan aka same shi da laifi, zai iya fuskantar hukuncin dauri a gidan yari.