'Yan sanda sun hana bunburutu a Nigeria

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta sanar da haramta sayar da man fetur a jarkoki da aka fi sani da bumburutu a kasar.

Sifeto janar na 'yan sandan Najeriyar Solomon Arase ya bayar da umarni ga mataimakan sifeta janar na 'yan sanda na shiyya-shiyya da su kama masu bumburutun ne duba da irin wahalar da ake sha tare da hadarin da ke tare bumburutun.

Mista Solomon wanda ya bayar da umarnin a Abuja a ranar Litinin, ya kara da cewa baya ga wahalar da sana'ar bumburutun ke haifarwa masu sayan mai, hakan kuma na sanya wasu 'yan Najeriya da ba su bin doka sun rasa muhallansu sakamakon gobarar da ke faruwa saboda ajiyar man fetur a jarka.

Arase ya kara da cewa man fetur yana da saurin kamawa da wuta kuma idan har ba a kula da yadda ake adana shi ba, zai iya barazana ga mutane da muhalli da kuma yanayi.

A yayinda ya ke yiwa gidajen sayar da man fetur gargadin cewa kar su sayar da man a jarkoki, sifeta janar din na 'yan sanda ya kara da cewa za a kama masu bumburutun da kuma masu sayan man a wurinsu kuma doka zata hukunta su.