An harba tauraron dan adam Sentinel-1B

Hakkin mallakar hoto ESA

Hukumar kula da sararin samaniya ta Turai ta harba tauraron dan adam na biyu.

Tauraron mai sunan Sentinel-1B an harbashi ne daga yankin Guiana ta Faransa.

Wasu daga cikin ayyukan da tauraron zai yi sun hada da sa ido akan gurbata teku da jiragen ruwa ke haddasawa, da yanayin kankara a teku, da kuma sa ido kan filaye.

Sentinel-1B zai yi aiki ne tare da tauraron 1A Spacecraft wanda aka harba a shekarar 2014.

Dukkan taurarin biyu, Sentinel-1A da Spacecraft-1A na kan ginshiki daya ne, to sai dai sun raba da ma'auni 180.

Kuma su na iya zana taswirar duniya baki daya kowanne kwanaki 6.