Alhini kan hatsarin nukiliya a Ukraine

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An kunna kyandira da yin addu'oi a safiyar Talata.

A kasar Ukraine, ana gudanar da alhinin cika shekara talatin tun bayan hatsarin nukiliya mafi muni a duniya da ya auku a Chernobyl.

An kunna kyandira, kuma an yi addu'oi a safiyar Talata a daidai lokacin da lamarin ya auku cikin watan Afrilun 1986.

Lokacin da lamarin ya auku dai, tashar nukiliya ta Chernobyl ta rufta, kuma gubar nukiliya ta fantsama, har ta dangana da kan iyakar Ukraine, ta tsallaka zuwa cikin Rasha, da Belarus, da kuma wasu kasashen arewacin Turai.

An dauka dai lamarin ya tallafa wajen rushewar tarayyar Soviet.