Buhari ya gana da jami'an Bankin Duniya

Hakkin mallakar hoto Nigeria President Twitter
Image caption Shugaba Buhari yayin da yake ganawa da jami'an bankin duniya a fadarsa

Babbar daraktar bankin duniya na wata ziyara a Nigeria a ranar Laraba, inda ta gana da shugaban kasar Muhammadu Buhari da wasu manyan jami'an gwamnatinsa a Abuja.

Mrs Sri Mulyani Indrawati ta ce manufar ziyarar ita ce fahimtar irin kalubalen da tattalin arzikin kasar ya shiga.

Ziyarar dai na zuwa ne bayan da gwamnatin Najeriyar ta nemi bashin dala miliyan biyu daga Bankin na duniya, domin samar da kudaden aiwatar da wasu manyan ayyuka a kasafin kudi bana.

Haruna Shehu Tangaza yana fadar shugaban Najeriyar a lokacin, ga kuma karin bayanin da ta yi wa su manema labarai bayan kammala ganawar:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti