Yawan yara masu teɓa ya karu a China

Hakkin mallakar hoto
Image caption Yara maza sun fi teba a China fiye da mata

An sami gagarumin karin yawan yaran da ke fama da teɓa a wasu sassan ƙasar China.

Wani bincike da ka gudanar kan yara 'yan makaranta dubu 28 da ke zaune a yankin Shandong a tsakiyar China, ya nuna cewa kusan kashi 17 cikin 100 na yara maza da kuma kashi tara cikin 100 na yara mata ne suke da tebar da za ta iya cutarwa a shekarar 2014.

Wanda adadi ya ƙaru matuka gaya idan aka hada da ƙasa da kashi ɗaya na yara maza da mata da suke da teɓa sosai a shekarar 1985.

Teɓa tsakanin yara ta zama wata babbar matsala a China, amma alamu sun nuna cewar yanayin abincin da ake ci a kasar ne ya sauya ta inda yanzu aka fi cin abinci mai dauke da sinadaran sanya kiba sosai.

Yara maza sun fi mata yin teɓa sosai a China, saboda a al'adance sun fi samun gata a gidajensu.