An daure 'yan jarida a Iran

Hakkin mallakar hoto TASNIM

Wata kungiya da ke sa ido kan harkokin kafofin yada labarai da ke Amurka, ta yi Allah wadai da hukuncin da wata kotu a Iran ta yankewa wasu 'yan jarida masu fafutukar kawo sauyi na zama a gidan yari tsakanin shekara biyar zuwa 10.

An kama Afarin Chitsaz da Ehsan Mazandarani da Saman Safarzai da kuma Davud Asadi da laifukan da suka hada da kin goyon bayan jami'an tsaron kasar.

An kama mutanen su hudu ne a a wani kame na masu tsattsauran ra'ayi da aka yi a watan Nuwamba.

Kwamitin da ke kare 'yan jarida ya bukaci Iran ta sauya dokokin da suka yarda a muzgunawa 'yan jarida.

An kuma tsare wasu marubuta da mawaka da kuma wasu a lokacin zaben 'yan majalisar dokoki da kuma kwararru a kan harkar majalisa inda magoya bayan shugaba Hassan Rouhani suka yi Nasara.