"Za mu kawo karshen barayin mutane a Kaduna"

Image caption Malam El-Rufa'i ya ce nan ba da dadewa ba za a kawo karshen wannan ta'asa

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce tana kokarin ganin al'amura sun daidaita ta fuskar tsaro bayan da a kwanan nan aka yi ta samun matsalar garkuwa da jama'a don neman kudin fansa da kuma barayin shanu.

Gwamnatin jihar ta rabawa jami'an tsaro babura domin inganta sintiri, ta kuma ce kokarinta shi ne ganin bayan barayin shanun da suka koma sace jama'a don neman kudin fansa.

An dai rabawa jami'an tsaro da suka hada da 'yan sanda da sojoji da jami'an kare afkuwar hadura ta kasa wato FRSC babura 51 don yin wannan aiki.

Gwamnan jihar Malam Nasiru El-Rufa'i ya ce, "In shaa Allahu nan ba da dadewa ba za mu kawo karshen irin wadannan ayyukan ta'addanci a jihar Kaduna da kewaye."

Yawanci maharan na aikata ayyukansu ne a dazukan Birni-Gwari inda nan maboyarsu take