Majalisa da NEMA za su tallafawa 'yan gudun hijira

Hakkin mallakar hoto AP

Majalisar Wakilai ta Najeriya da hadin gwiwar hukumar ba da agajin gaggawa NEMA, ta soma wani yunkuri na gano 'yan gudun hijirar rikicin Boko Haram wadanda ba a sansanoni suke ba.

Wannan tsari dai zai bada damar samar da tallafi ga 'yan gudun hijira masu yawan gaske da a baya ba a san da su ba.

An mika tallafin ga wasu daga cikin irin wadannan 'yan gudun hijira da ke jihar Jigawa.

Tun dai soma rikicin Boko Haram, yau shekaru 6 kenan, da dama daga cikin 'yan gudun hijirar na tsugunne ne a cikin jama'a ba a sansanoni ba.