Cutar komfuta ta harbi tashar nikiliyar Jamus.

Hakkin mallakar hoto THINKSTOCK

An samu kwayoyin cutar komfuta a cikin wayoyin USB da kuma na'urorin komfuta da aka yi amfani da su a tashar nukiliyar kasar Jamus .

An dai samu kwayoyin cutar a komfutocin ofishin da ake amfani da su wajen sarrafa yadda ake mulmula karafan dake ciyar da tashar nukiliyar.

Masana'antar samar da makamashi ta RWE ta ce kwayoyin cutar ba za su yiwa tashar nikiliyar wata illa ba, saboda masarrafar na'urorin ba su da alaka da yanar gizo, saboda haka ba za su iya yin tasiri ba.

Ma'aikatan tashar nukiliyar sun gano kwayoyin cutar komfutar ne a yayin da suke shirin kara inganta masarrafar sashe na biyu na tashar, da a yanzu ba ya samar da makamashi saboda wasu gyare-gyare da ake yi.

Yanzu haka na'urorin komfuta dubu daya ne aka gudanar da bincike a kan su don raba su da kwayoyin cutar, kana tashar ta kara inganta tsaron lafiyar na'urorinta.