'Yan gudun hijrar Damasak na bukatar agaji'

A farkon wannan makon ne gobara ta kona akalla gidajen kara 114 a sansanin 'yan gudun hijirar Gagamari a Jihar Diffa a jamhuriyar Nijar.

Yan gudun hijirar dai wadanda rikicin Boko Haram ya sa suka tsere daga garin Damasak na jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya ne.

Kananan yara uku ne aka bayyana cewa sun rasa rayukansu a gobarar.

Ɗan majalisar dattawan Najeriya mai wakiltar arewacin Bornon, Sanata Habu Kyari, ya buƙaci hukumomin Najeriyar da su gaggauta kai agaji ga ƴan gudun hijirar.

Daruruwan kananan yara 'yan makaranta ne dai mayakan Boko Haram suka yi awon gaba da su daga garin na Damasak, a cikin irin munanan hare-haren da suka sha kai wa.