Za mu dakile farautar giwaye a Afirka — Kenyatta

Shugabannin kasashen Afirka da dama ne ake za su gudanar da taron koli a kasar Kenya, kan matsalar farautar giwaye don fataucin haurensu.

Za su hallara a garin Nanyuki dake takiyar kasar Kenya karkashin wata kungiya da suka kafa 'Giants Club' , don tattauna yadda za a kare giwayen daga bacewa daga doron kasa.

Shugabannin za su gana da jami'an raya gandun dazauka, da shugabannin yan kasuwa daga kasashen duniya, da masana kimiyya, don tattaunawa kan yadda za a kawo karshen farautar giwayen.

Gabanin taron kolin Shugaba Uhuru Kenyatta na kasar Kenyar ya bukaci daukar tsauraran matakai na hana yin haramtaccen fataucin hauren giwayen.

Masu bincike sun ce kasashen Afirka na da kashi goma kacal na yawan adadin giwayen da suke da su a da kusan karni guda da ya wuce.

Sun kididdige cewa a ko wace shekara ana hallaka giwaye dubu talatin zuwa arba'in a nahiyar don samun hauren su.

A wannan adadi za a iya cewa nan da yan shekaru masu zuwa, giwayen za su iya bacewa daga doron kasa muddin ba a dauki matakan kawo karshen haramtacciyar farautar ba.