Ribar Facebook ta ninka sau uku

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masu amfani da Facebook na ci gaba da karuwa.

Ribar Facebook ta ninka sau uku a watanni hudu na farkon shekarar 2016, inda ya samu ribar dala biliyan 1.51.

Kudaden shiga da kamfanin ke samu daga yin tallace-tallace sun karu zuwa dala biliyan 5.2 inda kashi 80 cikin 100 na ribar ya fito daga sayar da wayar komai-da-ruwanka.

Yawan masu amfani da Facebook na ci gaba da karuwa.

Kamfanin Facebook ya mayar da hankali kan manhajar hoton bidiyo ta kai-tsaye wanda hakan ya jawo sababbin masu yin talla a kan shafin Facebook din yayin da yake ci gaba da yin ciniki na sauran manhajojin da da ma yake da su.

Shugaban Facebook, Mark Zuckerberg, ya kuma bukaci a fito da sababbin hannayen jari ta yadda zai iya bayar da sadaka yayin da yake ci gaba da jagorantar kamfanin da ya samar.

Kamfanin ya ce "Hakan zai karfafa wa Mista Zuckerberg gwiwar ci gaba da shugabanci a Facebook."

Ribar da kamfanin ya samu ta wuce yawan ribar da kasuwar hannayen jari da ke Wall Street ta yi zaton zai samu da fiye da kashi tara cikin 100.