Matsalar gurbatar muhalli a Najeriya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Najeriya na bukatar gaggauta shawo kan matsalolin dake gurbatar muhalli

Gidauniyar kula da muhalli ta Jamus a Najeriya, HBS, ta ce ƙasashe da dama a nahiyar Afirka sun yi wa Najeriyar fintinkau wajen rungumar makamashi maras gurbata Muhalli.

Wasu dai na ganin cewa akwai bukatar Najeriya ta gaggauta shawo kan matsalolin gurbatar muhalli, ta hanyar amfani makamashin da ba ya gurbata muhallin.

Sai dai kuma a cewar wasu masana harkar makamashi a Najeriyar, hanya daya ce tilo za ta fidda ƙasar daga wannan yanayi.

A cewar Farfesa Abubakar Sani Sambo, tsohon darekta janar na hukumar makamashi ta Najeriya, yin doka ne kawai zai sanya 'yan Najeriya su yi rungumi makamashin da ba ya gurbata muhallin.