An kai gawar Papa Wemba Congo

An kai gawar Papa Wemba, daya daga cikin shahararrun mawakan Africa wanda ya mutu ranar Lahadi a Ivory coast, Jamhuriyar Dimokradiyar Congo.

Daruruwan mutane ne suka taru a filin jirgin saman Kinshasa domin tarbar gawarsa.

An hada wani bikin rawa wanda aka kwashe daren ranar Laraba ana yi a birnin Abidjan inda ya fadi a lokacin da yake waka a kan dandamali, sannan daga bisani ya mutu.

Za a binne shi ranar Talata bayan an bai wa mutane damar ganin gawarsa a fillin wasanni da ke Kinshasa, babban birnin kasar.

Rahotanni sun ce jami'an gwamnati da na diflomasiyya za su halarci taron wake-wake da za a yi a filin jirgin saman kafin a kai gawar dakin ajiye gawarwaki.