Rabuwar kawuna tsakanin 'yan Shi'a a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sheikh Saleh ya ce kawunan 'yan Shi'a a rabe suke.

Wani reshe na kungiyar Shi'a mai suna Rasulul A'azam Foundation ya nesanta kan sa da abin da kungiyar 'yan uwa musulmi mabiya Malam Ibrahim Zakzaky suke yi da sunan Shi'a.

Ya ce akidar Shi'a ta ainihi ba ta yarda da sabawa dokokin da hukumomi suka sanya ba.

Reshen kungiyar dai ya shirya wani taron tattaunawa ne da jami'an tsaro kan yadda za a kaucewa irin rikicin da ya faru a Zaria cikin watan Disambar bara tsakanin magoya bayan Malam Ibrahim Zakzaky da kuma sojoji.

Shugaban kungiyar, Malam Nura Dass, ya shaida wa BBC cewa suna biyayya ga tsarin mulkin Najeriya da hukumominta:

Ya kara da cewa: "Malaman mu sun yi mana umarni mu bi doka da oda domin kasa ba ta zama lafiya idan ba a bi doka da oda ba.Ba mu yarda mu shiga Masallatai a rika yin rigima da mu ba".

Shi ma Sheikh Saleh Zaria ya ce yawancin mabiya Shi'a a Najeriya ba su san ainihin akidar ba, yana mai cewa hakan yana bata sunan masu akidar ta asali.

Ya kara da cewa akwai rabuwar kai tsakanin 'yan Shia.