Dan Amurka zai sha dauri a Koriya ta Arewa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kim Dong-chul ya amince cewa shi dan leken asiri ne.

Kasar Koriya ta Arewa ta yanke hukuncin daurin shekara goma tare da yin aiki mai tsanani kan wani dan kasar Amurka saboda yin leken asiri.

An kama Kim Dong-chul, mai shekara 62 wanda dan Amurka ne amma haifaffen Koriya ta Kudu, a watan Oktoban da ya gabata.

Kim ya shaida wa manema labarai a watan jiya cewa shi dan leken asiri ne, yana mai cewa jami'an leken asirin Koriya ta Kudu ne suka dauke shi aiki.

A baya dai Amurka ta zargi Koriya ta Arewa da musgunawa 'yan kasarta, sai dai Koriya ta Kudun ta musanta zargin.