Ana ci gaba da jimamin rasuwar Oba na Benin

Hakkin mallakar hoto twitter
Image caption Oba ya rasu yana da shekara 93

Ana ci gaba da jimamin rasuwar basaraken gargajiyar masarautar Benin, Oba Omo n'Oba n'Edo Uku Akpolopkolo Erediauwa a birnin Benin na jihar Edo kudancin Nigeria.

Shugaban majalisar sarakuna ta masarautar Benin Chief Sam Igbe, shi ne ya sanar da mutuwar a ranar Juma'a.

An gabatar da wasu abubuwa na al'ada a fadar domin a nuna tabbacin mutuwarsa.

Tuni gwamnatin jihar Edo ta fitar da wata sanarwa tana mai nuna alhininta kan wannan rashi.

Oba Omo n'Oba n'Edo Uku Akpolopkolo Erediauwa ya mutu yana da shekara 93 a duniya, inda ya shafe shekaru 37 a karagar mulkin masarautar.

Har yanzu dai ba a sanar da lokacin da za a yi jana'izar basaraken ba.