Sabon rikici ya ɓarke a PDP kan shugabanci

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jam'iyyar PDP tana shan fama da rikice-rikice tun bayan faduwarta zabe a shekarar 2015

Wani sabon rikici ya sake ɓarkewa a babbar jam'iyyar adawa ta Nigeria PDP, sakamakon kebe kujerar shugabanta na kasa ga shiyar arewa-maso-gabas, yankin da shugabanta na riko ya fito.

Jiga-jigan jam'iyyar daga shiyyar kudu-maso-yamma sun yi barazanar ficewa daga jam'iyyar idan ba a bayar da kujerar shugabancin jam'iyyar ga shiyyarsu ba.

An dai cimma wannan ƙudurin ne a yayin taron majalisar zartarwar jam'iyyar karo na 70 da aka yi ranar Alhamis.

A watan Mayu ne dai jam'iyyar ke shirin gudanar da babban taronta na kasa domin zabar sabbin shugabanni.

Ga rahoton da Haruna Shehu Tangaza ya hada mana:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti