An ceto zakuna 33 daga masu wasa da dabbobi

An kubutar da wasu zakuna 33 daga hannun mutanen dake wasa da dabbobi a kasashen Peru da Colombia inda aka kwashe su zuwa kasar Afrika ta Kudu.

Zakunan za su ci gaba da rayuwa a wani wuri da aka killace a kasar.

Kungiyar kare dabbobi ta Animal Defenders International da ke Amurka ce ta dauki nauyin kwashe dabbobin, bayan ta shafe shekaru tana aiki da 'yan Majalisun dokoki na kasashen.

Burin ta dai shi ne don ta ga an haramta amfani da dabbobi masu hadari wajen yin wasanni.

Kungiyar dai ta kwashe zakuna ashirin da hudu ne a kasar Peru yayin da guda tara kuma daga Colombia.

Wakiliyar BBC ta ce akasarin zakuna dai an yi ta gallaza muzu inda galibin su aka cire musu hakora.