Za a yi wa Zuma shari'a kan cin hanci

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Jam'iyyar hamayya ta Democratic Alliance, wacce ita ce ta shigar da kara a wancan lokaci, ta yi maraba da hukuncin kotun.

Wata babbar kotun Afirka ta kudu ta bukaci a sake fara bincike kan shugaban kasar Jacob Zuma game da zarge-zargen cin hanci da ake yi masa.

A shekarar 2009 ne aka wanke Mista Zuma daga zarge-zargen aikata laifuka 783 wadanda suka danganci cin hanci, lamarin da ya ba shi damar tsayawa takarar shugabancin kasar a wancan lokacin.

Sai dai alkalin babbar kotun Aubrey Ledwaba ya ce wanke shi daga zarge-zargen da aka yi bai dace ba, yana mai bukatar a sake fara gudanar da shari'a kan batun.

Jam'iyyar hamayya ta Democratic Alliance, wacce ita ce ta shigar da kara a wancan lokaci, ta yi maraba da hukuncin kotun.