Shugaban Kenya ya kona dubban hauren Giwa

Hakkin mallakar hoto AFP

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya kaddamar da kona dubban hauren Giwa da na Karkanda a karshen taron koli domin kawo karshen haramtaccen halayyar kashe dabbobin.

Da yake jawabi wajen kona hauren a babban gandun daji da ke Nairobi, shugaban kasar yace matakin wani gargadi ne ga daukacin duniya cewa wajibi ne a kawo karshen cinikin hauren Giwa.

Mr Kenyatta yace kasar Kenya za ta bukaci haramta sayar da hauren Giwa a duniya baki daya idan aka zo taron kasa da kasa kan kudiri kare cinikin tsirai da dabbobin daji da ke fuskantar barazanar bacewa wanda za a yi cikin wannan shekarar a Afirka ta Kudu.

Shekaru goma da suka wuce an sami matukar raguwar yawan giwaye a Afirka lamarin da ke barazana ga wanzuwa da kuma makomarsu a nan gaba.