Kwale kwale ya kife da yan gudun hijira a Libya

Hakkin mallakar hoto Libyan Coastguard

Kungiyar kula da kaurar jama'a ta duniya ta ce yan gudun hijira 84 sun bace ba a gano su ba, bayan da kwale kwalen da suke ciki ya kife a tekun Libya.

Sojin ruwan Italiya sun ce an ceto wasu yan gudun hijrar 26 yayinda su ma na su kwale kwalen ya nutse a teku a yankin Sabrata na kasar Libya.

Yan gudun hijira kimanin dubu 27 ne suka Italiya ta kwale kwale a bana.

Jamiai sun ce su na tsammanin yawan wadanda ke neman tsallaka tekun zai karu saboda kasashen yankin Balkans sun rufe kan iyakokinsu.