An kai hare-hare kan 'yan tawayen Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojojin gwamnati sun kai hari kan tawaye a Syria

An kai wasu hare-hare ta sama a gundumar da 'yan tawaye su ke a birnin Aleppo.

Masu fafutuka sun ce an kai hare-hare a yankuna uku inda 'yan tawayen ke rike da su.

Wannan dai shi ne fadan daya fi kowanne a birnin na Aleppo tun bayan fara yakin a 'yan kwanakin nan, al'amarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da dari biyu suka rasa rayukansu sakamakon hare-hare ta saman da dakarun gwamnati ke kaiwa kan tawaye.

Birnin dai baya cikin yarjejeniyar wucin gadi ta tsagaita wuta da sojojin Syria suka yi alkawarin tsagaitawa.

An dai bayar da rahotannin cewa an tsagaita wuta a wasu yankuna na kasar ta Syria.