Sabon tsarin kafafen watsa labarai a Najeriya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kafofin watsa labarai na rediyo da telibijin za su rika amfani da na'urorin zamani wajen watsa shirye-shirye

A Najeriya, an kaddamar da fara aiki da tsarin watsa shirye-shiryen rediyo da telibijin ta amfani da na'urorin zamani maimakon amfani da tsofaffin kayayyaki.

Ministan watsa labarai na kasar ne ya jagoranci kaddamar da shirin a birnin Jos na jihar Filato, daga nan kuma sai wasu jihohi su bi sahu, yadda za a tabbatar da tsarin ya karade kasar nan da watan Yunin badi.

Tsarin dai na nufin kafofin watsa labarai na rediyo da telibijin za su rika amfani da na'urorin zamani wajen watsa shirye-shiryen su.

Kazalika masu kallo da saurare wajibi ne su mallaki na'urorin zamani kafin su iya kallon telbijin ko sauraron rediyo a Najeriya.