Muna shirin kawo karshen fadan Syria- Amurka

Hakkin mallakar hoto AFP

Amurka na gudanar da wasu tsare-tsaren yadda za a shawo kan fadan da ya rincabe a Syria, tare da kawo karshen rashin jituwar da ke faruwa.

Ofishin huddar jakadancin Amurkar ya ce babban muhimmin abu shine dakatar da zub da jini a birnin Aleppo, inda mutane fiye da 200 suka hallaka a hare-hare ta saman da dakarun gwamnati ke kai wa, da kuma lugudan wutar 'yan tawaye ke yi.

Amurkar na nanata yin kira ga kasar Russia ta yi wa gwamnatin Syria matsin lamba na ta dakatar da abinda ta ce lugudan wutar ta ko ina .

Sai dai Rashar ta tsaya kai da fata cewa samamen ta sama kan birnin Aleepo a kan kungiyoyin 'yan ta'adda ne.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya nuna matukar damuwarsa kan kazancewar tashin hankalin na birnin Aleppo.

An bada rahoton cewa hari ta saman da dakarun gwamnati suka sake kai wa ranar Asabar ya hallaka akalla mutane hudu, tare da jikkata da dama.

Mr Kerry na dora alhakin fadan wanda ke karewa kan fareren hula kan shugaba Bashar al-Assad.