Shekaru 5 bayan kashe Osama bin Laden

Hakkin mallakar hoto AP

Hukumar leƙen asiri ta Amurka CIA, tana tuna cika shekaru 5 bayan kisan jagoran ƙungiyar Al Qaeda, Osama bin Laden.

CIA tana amfani da shafinta na Twitter wajen bayar da bayani dalla-dalla a kan samamen da ya kai ga kisan Osama bin Laden.

Zaratan dakarun Amurka ne suka kashe Osama bin Laden bayan sun dira ta jirgin sama a gidan da ya fake a Pakistan.

Shafin Twitter na CIA ya bayar da bayani daki-daki a kan samamen da ya kai ga kisan Osama bin Laden tamkar dai yanzu abin yake faruwa.

An kashe Osama bin Laden ne shekaru 10 bayan harin ranar 11 ga watan Satumbar shekara ta 2001, wanda ya bayar da umarnin kai wa.

Wakilin BBC kan harkokin tsaro ya ce, mutuwar Osama Bin Laden ta kawo ƙarshen ƙungiyar Al Qaeda, amma sai ƙungiyar IS ta maye gurbinta.