Fira ministan Iraki ya umurci a kame masu zanga zanga

Masu Zanga zanga a Iraki Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga zanga a birnin Bagadaza

Fira ministan Iraki,Haider al Abadi,ya umurci dakarun tsaron kasar akan su gurfanar da masu zanga zangar da suka lalata Majalisar Dokoki a gaban sharia.

Masu zanga zangar sun kuma kai wa jami'an tsaro da 'yan Majalisa hari a ranar Asabar.

Daruruwan masu zanga zangar har yanzu suna zaune a wajen Majalisar Dokokin da ke birnin Bagadaza.

Akasarin masu zanga- zangar magoya bayan malamin shi'a nan ne mai tsasauran ra'ayi Moqtada al Sadr.

Suna nuna fushi ne a kan gazawar Majalisar wajen amincewa da sauye - sauyen da za a yi wa tsarin siyasar kasar domin yaki da cin hanci da rashawa.