Najeriya: Sojoji sun gano abubuwa masu fashewa na BH

Boko Haram
Image caption Wurin da 'yan Boko Haram suke hada abubuwa masu fashewa

Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce ta bankado masana'antar hada abubuwa masu fashewa na kungiyar Boko Haram a garin Ngala a jihar Borno.

Ta ce ta gano wannan wuri ne sakamakon bayanan sirri da ta tattara kuma dakarunta sun lalata wurin tare da kashe wasu mayakan Boko Haram.

Kakakin rundunar sojin kasa,kanar Usman Sani Kukasheka ya ce sojojin sun gano tukunyar iskar gas guda ashirin da kuma sauran kayayakin da ake hada abubuwa masu fashewa.

A wani labarin kuma rundunar sojin kasa ta yi nasarar murkushe wani hari da mayakan kungiyar Boko Haram zasu kaiwa dakarunta da kuma farar hula a garin Wunbi da ke karamar hukumar Kala Balge a jihar Borno.

Ta ce dakarunta sun yi arangama da mayakan Boko Haram a kauyen Tatakura me nisan kilomita 20 da garin Wumbi bayan da suka samu bayanai akan harin.

Rundunar sojin ta ce dakarunta sun yi musayyar wuta sosai da 'yan ta'adan inda aka kashe mayakan Boko Haram 9.