Za mu cigaba da neman mai a arewa — Kachikwu

Hakkin mallakar hoto NNPC

Karamin minista a ma'aikatar mai ta Nigeria, Ibe Kachikwu ya ce, babu ja da baya dangane da neman mai da iskar gas a yankin arewacin kasar kusa da tafkin Chadi, da kuma yankin Benue.

Ministan ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ke ɗauke da sa hannun, Malam Garba Deen Muhammad, kakakin kamfanin mi na Njeriya, NNPC.

Ibe Kachikwu, wanda kuma shi ne shugaban kamfanin mai na ƙasa NNPC ya ce, an yi nisa wajen binciken da zai kai ga matakin soma haƙo mai a yankin tafkin Chadi.

Amma ya ce, rikicin Boko Haram ya tilasta dakatar da aikin a ranar 24 ga watan Nuwambar shekara ta 2014.

Ministan ya ƙara da cewa, gano mai a yankin tafkin Chadi zai ƙara yawan arzikin mai da iskar Gas da Nigeria ta mallaka.

Ya kuma ce, zai samar da dumbin ayyukan yi da kuma bunƙasa kasuwanci.

Ibe Kachikwu ya yi kira ga masu zuba jari na ƙasashen waje su sa hannu domin haɓaka dumbin arzikin mai da iskar gas da Nigeria take da shi.