An kashe sojoji a Somalia

Image caption Al Shabaab ta kashe sojojin Somalia fiye da talatin

Kungiyar masu kaifin kishin Islaman nan ta Al Shabaab ta ce ta kashe dakarun gwamnati fiye da talatin a lokacin da suka sake karbe ikon kauyen Runorgood wanda ke arewa maso gabashin babban birnin kasar Somalia Mogadishu.

Har yanzu dai ba a ji wani martani daga bangaren sojojin kasar ba.

Mazauna kauyen sun tabbatarwa da BBC cewa yanzu kauyen na Runorgood ya koma karkashin ikon Al Shabaab din.

A ranar Asabar din data gabata ne aka kori masu tayar da kayar bayan daga kauyen, amma kuma sun sake dawo da shi karkshin ikonsu a ranar Lahadi.

A wani labarin kuma a Somaliyan, wani harin bam da aka kai kan kasuwar dabbobi da ke Qoryoolay ya kashe mutane uku.