Somalia: Mutane 15 sun mutu a masallaci

Hakkin mallakar hoto Twitter

Mutane 15 sun mutu a Somalia yayin da wani masallaci da ake yiwa kwaskwarima ya rufta.

Wasu mutanen 40 da lamarin ya rutsa dasu sun jikkata.

Lamarin ya auku ne yayin sallar Juma'ar data gabata Mogadishu, babban birnin kasar.

Yayin da lamarin ya auku masallacin yana cike makil da masu ibada.

Har yanzu dai akwai wasu mutanen da ake zaton ginin ya rufta akansu.

Tuni aka kama injiniyan dake kula da aikin gyara masallacin bisa zargin yin sakaci.

Cikin 'yan kwanaki anyi ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a yankin da lamarin ya auku.