Turkiyya: An kai hari ofishin yan sanda

Hakkin mallakar hoto AFP

A kalla yan sanda biyu sun hallaka a wani harin kunar bakin wake da aka kai da wata karamar mota a wajen babban ofishin 'yan sanda a birnin Gaziantep a kudancin Turkiyya.

Mutane fiye da 20 sun sami raunuka wasu daga cikinsu fararen hula.

Yan sanda a Gaziantep sun yi wa gidan wani da ake zargi dan kungiyar IS ne kawanya wanda kuma ake kyautata tsammanin shine ya kai harin.

An tsare mahaifinsa domin gudanar da binciken kwayoyin hallita na DNA.

A shekarar da ta gabata Turkiyya ta fuskanci hare hare daga yan bindiga na kungiyar kurdawa da kuma IS.

A gefe guda kuma sojojin Turkiyya uku sun rasa rayukansu wasu 14 kuma suka jikkata yayin wani farmaki da suka kai kan yan tawayen Kurdawa a kudu maso gabashin gariin Nusaybin