Kungiyar direbobin dakon mai suna yajin aiki

Image caption Kungiyar kananann direbobin tankar man sun ce yajin aikin na kwanaki biyar ne

Kungiyar kananan direbobi masu dakon man fetur sun shiga wani yajin aiki na ba-za-ta a fadin Najeriya, saboda kisan wani mambansu da suke zargin jami'an hukumar kula da sufuri ta LASTMA a Lagos suka yi.

Kungiyar ta ce yajin aikin na kwanaki biyar wanda zai fara daga ranar Litinin zuwa Juma'a, na gargadi ne.

Ta kuma ce dole wadanda abin ya shafa su binciko dalilin kashe mambansu.

Batun tabbatar da zirga-zirga na gudana yadda ya kamata da kuma cincirindon tankokin mai, na daga cikin manyan kalubale da birnin Lagos ke fuskanta.

Daga Legas din wakilinmu Umar Shehu Elleman ya aiko ma na da wannan rahoto.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti