Mun kama wanda ya kashe Janar Shuwa - Sojoji

Hakkin mallakar hoto AP

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kama wani da take zargin ya kashe Manjo-Janar Mohammed Shuwa mai ritaya.

Kakakin rundunar sojin, Kanar Sani Usman Kukasheka ya fitar da wata sanarwa a shafinsa na Facebook, inda ya ce: "Jami'an sojin dake tattara bayanan sirri sun kama wadanda ake zargi da kisan Manjo-Janar Mohammed Shuwa, mai ritaya."

Ya kara da cewa "Kwamandan rundunar ta uku ta sojin Najeriya zai gabatar da shi gaban manema labarai a Kano, nan ba da dadewa ba."

Sai dai ba wannan ne karon farko da rundunar sojin Najeriyar ke bada sanarwar kama wadanda ake zargi da kashe Janar Shuwa mai ritaya ba.

Ko a shekarar 2012 ma, rundunar ta ce ta cafke wasu mutane uku da ta ce su ne suka kashe Janar Mohammed Shuwa.

Sai dai babu wani karin bayanin gurfanar da su a gaban alkali.

Marigayi Shuwa yana gaba-gaba cikin wadanda suka fafata a yakin basasar Najeriya.