Al'ummar Congo na alhinin mutuwar Papa Wemba

Hakkin mallakar hoto
Image caption An ajiye gawar Papa Wemba a majalisar dokokin kasar

Daruruwan mutane ne suka halarci taron nuna jimamin mutuwar shahararren mawakin nan na Afrika Papa Wemba, a kasar Congo.

Hukumomin kasar ne suka ware kwanaki uku na jimamin, wanda aka fara daga ranar Litinin zuwa ranar Laraba wadda za a binne shi.

An ajiye gawarsa a ginin majalisar dokoki da ke Kinshasa babban birnin kasar, inda daga baya za a mayar da shi zuwa garinsu domin jama'a su samu damar ganin gawar.

Shugaban kasar Joseph Kabila, da iyalan marigayin da kuma sauran mawaka duk sun halarci taron wanda ake yi a majalisar dokokin kasar.

Papa Wemba dai ya mutu ne bayan da ya fadi yayin da ya ke wasa a kasar Ivory Coast a makon da ya gabata.