Trump ya zargi China da yi wa Amurka zagon kasa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dama can Mista Trump ya sha sukar China

Dan takarar shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar Republican Donald Trump, ya zafafa sukar manufofin huldar kasuwancin China, yana zarginta da yi wa tattalin arzikin Amurka zagon kasa.

Yayin wani gangamin yakin neman zabe a jihar Indiana, Donald Trump yace, China tana yin abinda ya kira fashi da satar da ba a taba ganin irinsu ba a tarihin duniya.

Kuma yace, ba za a bari wannan lamari ya cigaba ba.

Donald Trump dai dama ya sha sukar China da manufofinta.