''Na yi umarni a ladabtar da makiyaya''

Hakkin mallakar hoto twitter
Image caption Shugaba Buhari yayin da yake ganawa da bishop-bishop

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari, ya jaddada aniyarsa ta kawo ƙarshen hare-haren da makiyaya ke kaiwa a kan wasu al'ummomin ƙasar.

Da yake magana yayin wata ganawa da ya yi da ƙungiyar bishop-bishop ta Najeriya, CBCN, Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa tuni ya bai wa shugabannin hukumomin tsaro umarnin ɗaukar matakan da suka dace da kuma bankaɗo duk mai hannu cikin wannan lamari.

Ya ce, ''A shirye muke mu kare duk 'yan Najeriya, kuma na shaidawa Sufeto Janar na 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro da murya mai ƙarfi cewa dole ne su hukunta maharan nan.''

Shugaban ya kuma miƙa saƙon ta'aziyarsa ga Bishop na cocin Katolika na Enugu da al'ummar Ukpabi Nimbo, kan rashin da suka yi sakamakon hare-haren da aka kai musu.

Cigaban kasa

Kazalika, ya yi tsokaci a kan al'amuran ƙasa, inda ya tabbatar wa da bishop-bishop ɗin cewa yana aiki ne a tsanake kuma yana taka-tsan-tsan domin ganin cewa ya cimma manufarsa ta kawo sauyi.

''Muna buƙatar yin komai a tsanake, muna kuma buƙatar sauya tsarinmu na gudanar da abubuwa,'' in ji shugaban.

Ya kuma tabbatar musu da cewa zai cika dukkan alƙawuran da ya ɗaukar wa 'yan Najeriya.

Reverend Ignatius Kaigama, wanda shi ne ya yi jawabi a madadin bishop-bishop ɗin, ya ce, ''A shirye muke mu bai wa shugaban ƙasa haɗin-kai, domin muna fatan zai kawo kyakkyawan sauyi a Najeriya.''

Matsalar hare-hare da ake zargi Fulani makiyaya da kaiwa dai ta fara ƙamari sosai a Najeriya, inda wasu ke ganin idan ba a tashi tsaye ba al'amarin zai iya zama wani abu daban.