'Gaɓar tekun Guinea ce wuri mafi hatsari a duniya'

Hakkin mallakar hoto
Image caption Rahoton ya ce 'yan fashin teku sun kawar da hankulansu daga kan satar tankunan mai saboda farashinsa ya fadi.

Wani sabon rahoto ya ce yankin yammacin Afirka na gaɓar tekun Guinea ya zama wuri mafi hatsari a duniya na masu safara a teku saboda karuwar hare-haren 'yan fashi.

Nazarin da wata kungiyar mai tushe a Amurka ta Oceans Beyond Piracy ta yi ya ce 'yan fashi a teku suna kara sace mutane domin karbar kudin fansa.

Rahoton ya kara da cewa faduwar farashin mai ta sa 'yan fashi a gaɓar tekun Guinea suna kawar da kai daga yi wa tankokin mai fashi.

Jami'an da ke gadin teku a Najeriya sun ce suna daukar matakan dakile wannan matsala.