Tattalin arzikin Afrika ya taɓarɓare

Asusun bayar da lamuni na duniya ya ce tattalin arzikin ƙasashen Afrika ya yi faduwar da bai taba yi ba a shekaru 15 da suka gabata, a cikin shekarar 2015.

Asusun bayar da lamunin ya kuma ce ana sa ran faduwar tattalin arzikin za ta tsananta a bana.

Taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasashen duniya sakamakon faɗuwar farashin kayan masarufi da kuma man fetur da annobar cutar Ebola, ya yi matuƙar shafar tattalin arziƙin ƙasashen Afrika.

IMF ya ce bunƙasar tattalin arziƙi Afrika kashi uku da rabi cikin 100 ne a bara, inda aka sa ran zai ƙaru da kashi uku cikin 100 a wannan shekarar.

Alƙaluman sun yi kasa sosai da kashi shida cikin 100 a shekara goma da ta gabata.