An ceto jaririya daga ginin da ya rufta a Kenya

Image caption Za a gurfanar da mutumin da ya mallaki ginin a gaban kotu.

An ceto wata jaririya 'yar shekara daya da rabi daga cikin baraguzai, kwana hudu bayan ruftawar da wani gini ya yi a birnin Nairobi na kasar Kenya.

Jaririyar na fama da karancin ruwa a jikinta, ko da ya ke babu wasu raunuka da aka gani a jikin nata.

Ginin, mai hawa shida, ya rufta ne sakamakon ruwan sama, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum 22.

Ana tsammani har yanzu akwai wasu mutanen a makale cikin ginin, ko da ya ke an fitar da ran samunsu a raye.

Tuni dai aka kama mutumin da ya mallaki ginin, kuma za a gurfanar da shi a gaban alkali ranar Talata bisa zargin kisan kai.