Wani abu ya fashe a Anaca

Hakkin mallakar hoto Nigeria Police website

A Najeriya, wani abu ya fashe a gefen wata kasuwa da ke birnin kasuwancin nan na Anaca a jihar Anambra, inda galibi 'yan arewacin kasar ke gudanar da harkokinsu.

Mutane akalla goma ne suka ji rauni, amma ba a sami asarar rai ko daya ba, kuma an kai jami'an tsaro da ke gudanar da sintiri a wajen.

'Yan sanda sun ce, suna ci gaba da bincike akan lamarin.

Wani shaida ya ce, mutane da dama sun gudu sun bar wurin da lamarin ya auku.