An sace $15b na sayen makamai a Nigeria — Osinbajo

Image caption An kashe dala biliyan 15 da sunan sayen makamai don yakar Boko Haram a Nigeria

Mataimakin shugaban kasar Nigeria Yemi Osinbajo, ya ce an sace kimanin dala biliyan 15 a karkashin gwamnatin kasar da ta gabata na sayen makaman gaibu.

Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana hakan ne a wajen taron kaddamar da wani littafi da aka wallafa a kan, "Abubuwan da ke kawo naƙasu ga tattalin arziƙin Nigeria,'' a birnin Ibadan.

Ya ce, ''A 'yan kwanakin da suka gabata ne aka gano cewar jumlar kudin da aka sace ta silar cin hanci da rashawa da sunan samar da kayan yaƙin soji sun kusa kai wa dala biliyan 15. Don haka yin la'akari da wadannan makudan kudi zai sa a fahimci cewa ba karamar ɓarna aka yi ba a ƙasar nan."

Mataimakin shugaban ƙasar ya ƙara da cewa, yawan wannan kuɗi da aka wawure ya wuce rabin asusun ajiyar ƙudaɗen waje na ƙasar kimanin dala biliyan 27.

Mista Osinbajo ya kuma ce, ''Na yi amanna cewar yana da muhimmanci na aike wannan saƙo ga al'umma, cewa ba bu wani ma'aikacin gwamnati da zai ci kuɗin gwamnati ya zaci ya ci bulus. Idan kunne ya ji, to jiki ya tsira.''

Kazalika, Farfesa Osinbajo ya ce nan ba da jimawa ba za a fara ayyukan da suka dace da kasafin kudin bana, wanda ba a taba yin mai yawa irinsa ba.

Kalaman mataimakin shugaban ƙasar sune na baya-bayan nan da gwamnati ta yi kan batun yakin da cin hanci rashawar da take yi.