Za a bai wa Turkiyya damar zuwa kasashen EU

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Mataimakin shugaban hukumar, Frans Timmermans

Hukumar Tarayyar Turai ta bayar da shawarar bai wa 'yan kasar Turkiyya damar zuwa da yawa daga cikin kasashen Tarayyar Turai ba tare da biza ba.

Wannan mataki na zuwa ne a wani ƙoƙari na aiki da muhimmiyar yarjejeniya a kan 'yan gudun hijira tare da Turkiyya.

Mataimakin shugaban hukumar, Frans Timmermans, ya ce da farko tilas ne Turkiyya ta cimma wasu muhimman sharruɗa da aka gicciya, amma tana kan hanyar kai wa gaci

Ya ce, ''Har yanzu akwai sauran aiki a matsayin wani abu na gaggawa, amma idan Turkiyya ta cigaba da yadda take tafiya to zata cimma sauran sharruɗan.''

Sauye-sauyen--waɗanda za su iya fara aiki a watan Yuli, na buƙatar amincewar da yawan mambobin tarayyar Turan da majalisar dokokin Turan, inda aka nuna shakku kan yadda Turkiyya ke tunkarar batun 'yancin bil adama.