Nijar: An soma rajistar maniyyata Hajjin bana

A Jamhuriyar Nijar, hukumar kula da aikin Hajji da Umra ta kasar, COHO ta kaddamar da rajistar maniyyata aikin Hajjin bana.

Hukumar ta bai wa kamfanonin aikin Hajjin kwanaki 30 domin yin rajistar alhazansu.

Tuni dai aka tantance kamfanoni biyu na jiragen sama da za su yi jigilar alhazan a wannan shekara.

Bana dai Saudiyya ta bai wa Nijar gurbin alhazai 12,712.

Sai dai kuma kasar ta Nijar tana neman karin kujerun aikin hajjin 1,500.