Za a kafa kotu kan 'yan Boko Haram

Hakkin mallakar hoto State House

Gwamnatocin Nigeria da Kamaru sun ce akwai buƙatar kafa wata kotu ta musamman da za a gurfanar da dubban mutanen da aka kama a ƙasashen biyu bisa tuhumar zama 'yan ƙungiyar Boko Haram.

Wannan dai na ƙunshe a cikin sanarwar bayan taron da aka fitar a ƙarshen ziyarar da shugaba Paul Biya ya kawo Najeriya.

Kungiyar Boko Haram na matsa kai hare-hare a kasashen biyu.

Najeriya da Kamaru sun kuma sanya hannu kan yarjeniyoyi daban-daban da suka shafi tattalin arziƙi da zamantakewa.

Haruna Shehu Tangaza ya halarci taron manema labarai da shugabannin biyu suka yi a ƙarshen ziyarar ga kuma rahotonsa daga Abuja:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti